Kamfanin Apple ya soma fadawa tasku

Hakkin mallakar hoto Apple store

Kamfanin Apple mai kera wayoyin komai da ruwan na iphone ya sanar da koma bayan ciniki da ya samu a karon farko cikin shekaru goma sha uku.

Apple din ya ce ya samu faduwa a harkokin cinikayyarsa ta kusan dala biliyan takwas ko kuma fam miliyan biyar da rabi idan aka kwatanta da bara.

Kana ya ce kasuwar hannayen jarinsa ta fadi da kusan kashi ashirin bisa dari a cikin watanni 12.

Da dama na kallon wannan batu kamar alamu ne cewa kambun nasarar da kamfanin na Apple ya rike na tsawon lokaci yanzu ba shi da tasiri.

Ben Wood wani masani kan harkokin masana'antun fasahar kere-kere ya ce Apple din zai iya farfado da cikinkinsa a kasuwa mai ci sosai ta kasar India.

Amma kuma ya ce akwai babban kalubale ga kamfanin wajen sayar da wayoyinsa na iPhones a kasar ta India a kan cikakken farashin da ya saba,.

Sai dai ba za a yanke kauna daga yawan al'umma da kawa-zucin amfani da wayoyin komai da ruwan kan ba.

Graham Seddon,wani masani kan fasahar sadarwa shi kuma na ganin tauraruwar wayoyin iPhones na kamfanin na gaf da dusashewa.