Ribar kamfanin Apple ta ragu

Hakkin mallakar hoto Getty

Kamfanin Apple ya sanar da cewa cinakin da ya ke ya ragu da kashi 13 cikin 100 a cikin watanni 6, saboda kasuwar iPhone ta yi kasa.

Kamfanin ya sanar da cewa cinakinsa ya ragu daga dala bilyan 58 zuwa dala bilyan 56 a shekarar da ta gabata.

Wanan shi ne karo na farko da kamfanin ya samu raguwar cinaki tun shekarar 2003.

Ana dai sayar da iPhone milyan 61.2 duk wata 3, a yayin da a shekara ta 2015 cinikin ya ragu zuwa iPhone milyan 51.2 cikin watanni 3.

Kamfanin na Apple na fuskantar rashin kasuwar ne saboda rashin cinaki da ake samu a China, wanda ya ragu da kashi 26 cikin 100.