Gizo-gizo ya ciji wani mutum a mazakuta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cizon gizo-gizo yana iya haddasa ciwo mai tsanani, da gumi da kuma tashin zuciya.

Wani mutum a kasar Australia ya kai kansa asibiti bayan wani gizo-gizo mai dafi ya cije shi a mazakutarsa.

Gizo-gizon ya ci ji mutumin ne a lokacin da yake yin ba-haya a wani ban-daki a birnin Sydney.

Wani mai magana da yawun asibitin St George ya tabbatar da cewa an bai wa mutumin, mai shekara 21, maganin kashe dafi.

Gizo-gizon da ya ciji mutumin dai yana da wata jar jela a kusa da duwawunsa.

Cizon gizo-gizo yana iya haddasa ciwo mai tsanani, da gumi da kuma tashin zuciya.