BH: Kasashen duniya basu cika alkawarin taimako ba

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi yayin wani taro

Kwamandan rundunar hadin gwiwa da ke yaki da kungiyar Boko Baram a yankin tafkin Chadi MNJTF, ya ce kasashen duniya na jan kafa wajen tabbatar da taimakon da suka yi wa rundunar alkawari.

Janar Lamidi Adeosun ya ce har yanzu ba su samu wani babban taimako ba daga abokan arzikin idan aka kwatanta da alkawarin da suka dauka.

Kwamandan na rundunar ta MNJTF ya yi wannan sukar ne yayin ziyarar aikin da ya kai kasa Nijar a farkon wannan makon.

Ya ce kawo yanzu kayayyakin da rundunar ta samu daga hannun abokan arzikin basu wuce 11 ba da suka hada da na'urori.

Janar Adeosun ya kara da cewa ya kamata kasashen duniyar su yi la'akari da cewa har yanzu da sauran rina a kaba wajen murkushe kungiyar Boko Haram a yankin tafkin Chadi, ta yadda har yanzu ake bukatar taimakon abokan hulda na arziki.