Buhari ya yi Allah-wadai da harin Enugu

Image caption Ana zargin Fulani makiyaya da kai wannan hari

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya bai wa jami'an tsaro umarnin su gano wadanda ke da alhakin harin da aka kai a kan al'ummar Ukpabu Nimbo dake yankin Uzo-Uwani a jihar Enugu a ranar Litinin.

Shugaban ya bada umarnin ne a cikin jawabinsa, wanda ministan yada labarun kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya karanta a lokacin bikin kaddamar da wani littafi da mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeriar Sanata Ike Ekweremadu ya rubuta, a ranar Laraba a Abuja

Shugaban ya ce yana matukar tausayawa wadanda harin ya shafa da kuma wadanda suka rasa dukiyoyinsu.

Ya ce '"Na bai wa babban hafsan tsaro da kuma sufeta janar na 'yan sanda umarnin su tabbatar da tsaro a dukkanin al'ummomin da suka fuskanci hare-haren makiyaya, sannan su yi maganin dukkanin kungiyoyin mutanen da suke musgunawa mutane a dukkanin fadin kasar.

Shugaban ya kara da cewa "gwamnati ba za ta kyale wadannan hare-hare su ci gaba da faruwa ba".