EFCC ta kwace gwala-gwalan N593m na Diezani

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Diezani da sace makudan kudade daga kamfanin NNPC.

Hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC ta kwace gwala-gwalan da darajarsu ta kai miliyoyin naira daga hannun tsohuwar ministar mai, Diezani Alison Madueke da kuma matar wani makusancin tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren wanda ya tabbatar wa da BBC labarin ya ce yanzu haka hukumar na cigaba da bincike a kan tsohuwar ministar.

Sai dai bai bayyana darajar gwala-gwalan da EFCC ta kwace ba, ko da yake wata kafar watsa labarai ta kasar ta ce darajar gwala-gwalan da kuma wani agogon hannu ya kai fiya da naira miliyan 593.

A baya-bayan nan ne dai hukumar binciken manyan laifuka ta Birtaniya NCA ta gudanar da wani bincike a kan Diezani Alison-Madueke

A shekarar 2014 ne kuma tsohon shugaban babban bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi, ya zargi babban kamfanin man fetur na Najeriya, wanda Diezani ke shugabanta, da kin saka $20 biliyan a lalitar gwamnatin tarayya kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yaki cin hanci da rashawa musamman a bangaren man fetur na kasar.