'Hankalinmu ya tashi kan dokar hana bara'

A Nijeriya wasu malamai na nuna adawa da dokar da gwamnatin jahar Kaduna ta kafa na hana bara da kuma bayar da sadaka a kan titina.

Dokar dai ta tanadi horo ko tara ga duk wanda ya yi bara da ma wanda ya bada sadaka a titinan jihar.

Malaman dai sun ce sanarwar da gwamnatin ta yi game da dokar ta kidima su.

Sai dai gwamnatin ta ce babu gudu babu ja da baya game da aiwatar da dokar.

Ta kuma ce bara ba addini ba ce kamar yadda wasu ke dauka.

Gwamnatin dai ta ce ta mikawa majalisar dokokin jahar bukatar kafa wannan doka,kuma tuni ta amince ta ita ta kuma mika mata don aiwatarwa.