An koka kan auren dole a Nijar

Image caption Masana sun ce ana yin auren dole ne saboda kwadayin abin duniya.

Wani rahoto da kungiyar Amnesty International ta fitar ya ce Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen Afrika ta yamma inda har yanzu ake fama da matsalar auren dole.

Kungiyar ta ce ana yi wa yaya mata auren tun shekarunsu ba su kai ba.

A cewarta, lamarin na tattare da matsaloli masu dama ga rayuwar matan.

Shugabar hadin gwiwar kungiyiyon mata na kasar, Madam Kako Fatima, ta shaida wa BBC cewa ana aurar da mata da wuri ne saboda talauci da al'ada, yayin da ake yi musu auren dole saboda kwadayin abin duniya.

Kungiyoyin sun yi kira a samar da dokokin da za su hukunta iyayen da ke yi wa 'ya'yansu auren wuri da na dole.