An mika wa Faransa Salah Abdeslam

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutum 130 suka mutu a harin na Paris.

Hukumomi a kasar Belgium sun mika wa kasar Faransa Salah Abdeslam, mutumin da ake zargi da kai hari a birnin Paris domin ya fuskanci hukunci.

An ji masa rauni a lokacin samamen da aka kai ranar 18 ga watan Maris a wurin da ya buya a birnin Brussels, bayan ya kashe wata hudu yana buya.

An haifi Abdeslam, mai shekara 26, a birnin na Brussels, kuma a can yake zaune kafin kafin harin da aka kai a Paris.

Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutum 130 da jikkata mutanen da dama a harin, wanda 'yan kungiyar IS suka kai ranar 13 ga watan Nuwamba.