Rasha na ci gaba da yaki a Syria

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti

Yayin da aka ga duk wasu alamu da ke nuna cewa an samu cikas a tsagaita wuta a Syria da kuma matsala a tataunawar zaman lafiyar kasar, rundunar sojin Rasha da kawayenta na Syria na kara kaimi wajen shirin kai sabon farmaki a ciki da kuma wajen birnin Aleppo

A makon da ya gabata, ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce dakarun da ke goyawa gwamnatin Syria baya sun soma tattara karfinsu a wuraren birnin Aleppo.

Mai magana da yawun Amurka ya ce 'Kungiyar al-Nusra ce ke rike da Aleppo kuma al-Nusran bata cikin kungiyoyin da suka dakatar da bude wuta. A saboda haka abinda sarkakiya. Muna zura ido.''

A tsakiyar watan Maris, Shugaba Vladimir Putin ya sanar da cewa Rasha za ta soma janye sojojinta daga Syria.

Abinda ya sa kusan rabin jiragen saman da ta jibge a kasar suka bar sansanin sojin saman Rashar da ke kusa da Latakia.

Sai dai tashinsu, bai kawo karshen farmakin da sojojin Rashan ke kai wa ba.

Hakkin mallakar hoto AFP

"Cigaba da luguden wuta"

Rashan ta ci gaba da luguden wuta, a yanzu ma hakan ya karu da isowar wasu jirage na baya-bayan nan masu saukar ungulu, wadanda take amfani da su wajen kaddamar da hare-haren soji- wato Ka-52 da kuma Mi-28N.

To shin me yake faruwa? Me ya canza bayan janyewar Rasha? Kuma me yasa Rashan take kaddamar da wasu sabbin farmaki?

A halin da ake ciki, har yanzu goyan bayan da Rasha take bai wa Shugaba Assad na nan daram.

Rasha na bukatar ta kara karfin matsayin gwamnatin Syria- amma bata son ta kasance a fagen daga a Syria har abada.

Hakkin mallakar hoto AFP

Me Rasha ta cimma a Syria?

. Jirgin saman Rasha ya jibge dakaru fiye da 9,000 . Rasha ta lalata kayayyakin samar da mai da kuma tura shi guda 209 . Ta taimakawa dakarun Syria sake kwace yankuna 400 . Ta taimakawa Damascus sake karbe iko da yankinta mai fiye da murabba'in kilomita 10,000