An bukaci Amurka da Rasha su sa baki a Syria

Hakkin mallakar hoto Getty

Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan De Mistura ya yi kira ga Amurka da Rasha da su ceto tattaunawar sulhun da ke neman rushewa a kasar.

Da yake magana jim kadan bayan jawabi ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar, De Mistura ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar na tangal-tangal, ta yadda za ta iya wargajewa a ko wane lokaci.

Ya kara da cewa mutuntakar Barack Obama da shugaba Vladimir Putin ta danganta ga samun nasarar shirin tattaunawar zaman lafiyar a Syria.

Ya ce muddin ana son a samu nasarar tattaunawar zaman lafiyar, to kamata ya yi a rage kaifin rashin jituwar dake tsakani, yana mai fatan a sake komawa kan teburin tattanawar a Geneva cikin watan Mayu.

Wakilin na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna takaicin yadda ake ci gaba da gwabza fada a kasar Syriya duk kuwa da zaman tattaunawar zaman lafiya a baya bayan nan.

A makon jiya ne dai manyan 'yan adawar kasar Syria suka fice daga zauren tattaunawar, inda suka yi barazanar kin dawowa zauren, matukar ba a kai karin kayayyakin agaji ba a yankunan da aka yi wa kawanya.