Ni ne zan yi wa Republican takara —Trump

Image caption Da alama Trump da Clinton ne za su fafata a zaben shugabancin Amurka.

Donald Trump ya ce shi ne zai tsaya takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican bayan ya lashe zaben fitar da gwani a jihohi biyar da aka yi ranar Talata.

Mista Trump ya lashe zaben ne a jihohin Connecticut, Delaware, Maryland, Pennsylvania da Rhode Island.

Ita ma matar da ke son yin takarar shugabancin kasar a karkashin jami'yyar Democrat, Hillary Clinton, ta lashe zaben jihohi hudu cikin biyar din da aka yi a ranar ta Talata.

Ta yi nasara a jihohin Connecticut, Delaware, Maryland, da Pennsylvania yayin da abokin takararta na Democrat, Bernie Sanders ya lashe zaben Rhode Island, kuma ya sha alwashin ba zai janye daga takarar ba.

Mista Trump ya lashe zaben ne duk kuwa da alwashin da abokan takararsa su,Ted Cruz da John Kasich, suka sha cewa za su yi masa taron-dangi domin ganin bai kai labari ba.

Ya shaida wa masu goyon bayansa a New York cewa ba zai sauya matsayinsa kan shirye-shiyen da ya sha alwashin kaddamarwa a Amurka ba, cikinsu har da korar Musulmai daga kasar.