Trump ya soki manufofin Obama na ƙasashen waje

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mista Trump ya soki Obama kan manufofinsa na kasashen waje

Mai neman takarar shugabancin ƙasar Amurka a ƙarƙashin jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya gabatar da jawabinbsa na farko a kan manufofinsa na ƙasashen waje.

Da yake gabatar da jawabin a birnin Washington, Mista Trump ya yi kakkausar suka a kan manufofin Shugaba Barack Obama na ƙasashen waje, waɗanda ya ce sun sa Amurka ta yi sako-sako.

Mista Trump ya ce yanzu lokaci ya yi da za a ɗaga darajar manufofin Amurka na ƙasashen waje a kuma sanya buƙatun ƴan kasar da na tsaro sama da komai.

Trump dai shi ne mai neman yi wa jami'iyyar adawa ta Republican takarar shugabancin ƙAsa a Amurka wanda ke da rinjaye a zaben fitar da gwani.

Karin bayani