An ba da umurnin a biya ma'aikata albashi a Bauchi

Hakkin mallakar hoto Bauchi State Govt
Image caption Ma'aikata a Bauchi sun shiga wani hali ne tun lokacin da gwamnatin jihar ta fara aikin tantance ma'aikata.

A Najeriya, Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta umarci babban akanta na jihar da ya biya dukkan ma'aikatan gwamnati da 'yan fansho da aka tantance su kudaden su na albashi da kuma fansho nan da ranar Juma'ar makon gobe.

Majalisar da baa umurnin ne bayan da babban akantan da wasu manyan jami'an gwamnati suka bayyana a gabanta game da kiki-kakar da ake fuskanta kan hakkokin ma'aikatan.

An shiga rudani da kunci a jihar ta Bauchi ne kan kudaden albashi da fansho tsawon watanni, yayin da gwamnatin jihar ke aikin tantance ma'aikatan.

Rahotanni sun ce hatta dubban ma'aikata da aka tantance sun yi ta korafin cewa ba a biya su hakkokin su ba.