An kai mummunan hari asibiti a Aleppo - MSF

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar likitoci ta Medecins sans Frontieres, MSF, ta ce a kalla marasa lafiya 14 da kuma likitoci uku ne suka rasa rayukansu a wani harin sama da a kai kan wani asibiti a birnin Aleppo da ke Syria.

MSF ta ce a cikin wadanda aka kashe a asibitin al-Quds da MSF ke tallafawa, har da kwararren likitan yara daya da ya rage.

Wasu majiyoyin kasar sun dora alhakin hakan kan gwamnatin Syria ko jiragen yakin Rasha, amma har yanzu hukumomin kasar basu ce komai a kan lamarin ba.

Masu sanya idanu sun ce bangarorin biyu sun yi sanadiyar mutuwar mutane 34 kuma mutane da dama sun jikkata a ranar Alhamis.

A baya-bayan nan dai rikicin Syrian ya kara tsananta duk da yarjejejniyar tsagaita wutar da aka sanyawa hannu.