An bukaci Cameron ya hana 'barayin' Nigeria zuwa Biritaniya

Image caption 'Yan Najeriya sun mayar da Biritaniya wajen zuwa su kashe makudan kudi don jin dadinsu

Ƙungiyoyin fararen hula a Nigeria sun yi kira ga Biritaniya ta hana mutanen da ake zargi da sace kudin kasar zuwa Ingila.

Ana dai zargin yawancin wadanda suka saci kudin Najeriya suna zuwa kasashen Turai da na Larabawa domin more rayuwarsu.

Amma a wata budaddiyar wasika da suka aikewa Firai ministan Biritaniyan, ƙungiyoyin sun ce suna so Mista Cameron ya ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki wajen kawo ƙarshen badaƙalar da wasu 'yan Najeriya ke zuwa ƙasarsa suna yi da dukiyar ƙasa da suka sata.

Ƙungiyoyin sun ce suna wannan kira ne a yayin da Mista Cameron ɗin ke shirin amsar baƙuncin shugabannin duniya a London, domin gudanar da taro kan yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ƙungiyoyin sun koka cewa Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka yi ƙamari wajen cin hanci, ta yadda ake sace kudin ƙasar a tafi ƙasashe irin su Biritaniya a kashe su wajen sayayyar almubazzaranci da kai yaransu makarantu masu tsada da kuma zuwa asibitoci.

Sun kuma tabbatar da cewa daga yanzu za su fara kamfe kan yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.

Wakilan kungiyoyin kimanin 95 ne suka rubuta wasikar.

Sayen gidaje da ajiya a banki, suna cikin hanyoyin halatta kudaden haram.