Nigeria da Faransa sun hada kai kan tsaro

Image caption Faransa za kuma ta bai wa sojojin Najeriya horo kan harkar tsaro

Najeriya da Faransa sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi na hadin kai da juna ta fuskar tsaro, ciki har da sayen makamai.

Ministocin tsaron ƙasashen biyu ne suka cimma yarjejeniyoyin a karshen taron farko na wani babban kwamitin hadin gwiwa a kan tsaro tsakanin Najeriya da Faransa, wanda aka yi a Abuja babban birnin Najeriya.

Kazalika, a bangaren bai wa sojoji horo, taron ya amince da tsara wasu kwasakwasai na bayar da horo ga sojojin Najeriya a kasar Faransa, da samar wa rundunonin sojin kumdumbalarta na kasa da na ruwa da kayan aiki.

Ministan tsaron Najeriya Mansur Muhammad Dan'ali ya ce taron wani sakamako ne na ziyarar da Shugaba Buhari ya kai kasar Faransa a watan Febrairu.

Haruna Shehu Tangaza ya halarci taron ga kuma rahotonsa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti