An tsawaita dokar ta-baci a Diffa

Hakkin mallakar hoto

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tsawaita dokar ta-baci a jihar Diffa zuwa wata uku.

A ranar Laraba ne dai gwamnatin kasar ta dauki wannan mataki a lokacin da ake wani zaman taron majalisar ministocin da shugaban kasar, Alhaji Muhammadou Issoufou.

Sun ce sun dauki matakin ne saboda hare-haren da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kai wa a yankin.

Mazauna yankin sun bayyana jin dadinsu da tsawaita dokar, suna masu cewa bukatarsu kawai ita ce a samu dawwamammen zaman lafiya a yankin.

Jihar ta Diffa dai na fama da hare-haren kungiyar Boko Haram, kasancewarta makwabciyar Najeriya.