Sudan ta kudu na bukatar zaman lafiya

A dakatar da yaki a daina kabilanci - muna bukatar alawa da Ice cream. Wannan shine abin da 'yan mata 'yan makarantar Firamare ta Juba ke bukata a wannan sabon karnin a Sudan ta kudu.

Komawar madugun 'yan tawaye Riek Marshar zuwa Juba ya bada dama ga 'yan Sudan ta kudu su yi tunanin kyakkyawar makoma a nan gaba, kwanciyar hankali da karuwar wadata a kasar.

Sai dai ko shakka babu, idan aka yi la'akari da halin kuncin yakin basasar kasar ya haifar da kuma tarihin rikice rikicen da suka faru a baya, akwai yiwuwar samun tashin hankali a gaba.

Labari mai dadi

Yanzu an rantsar da Mr Machar a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko, wanda ya share fagen cewa za'a iya kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Ana fatan gwamnatin za ta yi mulki na wa'adin wucin na watanni 30 lokacin da za a gudanar da zabe - tashin hankali da mai yiwuwa ake hange a gaba shine kudirin Mr Mcahar na zama shugaban kasa yayin da a waje guda kuma akwai yiwuwar shugaba Salva Kiir ya ki amincewa da haka.

Akwai bukatar hade sojojin da ke adawa zuwa rundunar soji ta kasa.

Wannan ba zai zama abu mai sauki ba ganin irin kallon hadarin kajin da sojojin gwamnati da na 'yan tawaye suka yiwa junansu a filin jirgin sama lokacin da Mr Machar ya sauka. Sun tsaya nesa da juna tare da kin nuna ban girma ga tsoffin bokan gabansu.

Sabuwar gwamnatin da za a kafa ana kuma sa ran za ta kafa kotun musamman domin shari'ar wadanda ake zargi da aikata mummunan ta'asa da kuma tsara shirin sasantawa da yafewa juna.

Abin da kamar wuyaDeja-VU

An jinkirta komawar Mr Machar bayan tsawon kwanaki ana takaddama wannan manuniya ce na rashin amincewar da ke tsakaninsu. Haka kuma babu wani karsashi da suka nuna lokacin da Mr Machar da Mr Kiir suka gaisa da juna a lokacin rantsar da Machar din.

Kar ta san kar

Mr Machar ya jagoranci wata kungiyar yan tawaye a 1991 lokacin gwagwarmaya da gwamnatin Sudan.

Daga baya ya koma ya bi sahu inda ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa ga Mr Kiir.

Tafiyar ba ta yi dadi ba kamar yadda wani Minista ya baiyana, yace Mr Kiir da Mr Machar kowannen su ya rika gudanar da aikinsa a kebe a cikin gwamnati.

Wannan rashin jituwar ce ta da ta yi kamari ta fito fili a 2013 lokacin da Mr Kiir ya kori mataimakinsa daga nan yaki ya barke bayan 'yan watanni.

Hakkin mallakar hoto Reuters