Zanga zangar dalibai a Sudan

Yansanda a Khartoum babban birnin kasar Sudan sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa dalibai da ke zanga zanga game da kisan wani dalibi dan uwansu a ranar Laraba.

Daruruwan daliban sun yi dandazo a tsakitar birnin abin da ba a saba gani ba kasancewar sun saba yin zanga zanga ne a kusa da tsangayoyin makarantunsu.

Hakan nan kuma sun yi zanga zangar a wajen Jami'ar Khartoum.

Dalibin ya rasu ne yayin zanga zangar adawa da shirin gwamnati na sayar da gine ginen jami'oi.

Mahukuntan Sudan galibi su kan mayar da martani ne da karfi yayin duk wata zanga zanga.