Mutane 55 ne suka mutu a harin Aleppo

Hakkin mallakar hoto no credit

Ma'aikatan agajin sa kai a birnin Aleppo na Syria sun ce akalla mutane 55 ne suka mutu a hari ta saman da aka kai a wani asibiti a daren Laraba.

Ma'aikatan kungiyar sa kan da aka fi sani da 'White Helmets' na cigaba da yin haka a cikin buraguzan ginin, sa'oi ashirin da hudu bayan lugudan wutar.

Mutane fiye da dari biyu ne aka bada rahotin sun hallaka a birnin na Aleppo a cikin makon da ya gabata sakamakon lugudan wuta da kuma haren-haren da dakarun gwamnatin ke kaiwa ta sama.

Shugaban kula da agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Stephen O'Brien ya bukaci kasashen Rasha da Amurka su ceto yarjejeniyar zaman lafiyar da ke neman rugujewa.

Ya ce ya kamata kasashen duniya su ji kunya kan abinda ke faruwa.