An tuhumi Amazon da sayar da manhajja ba tare da izni ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kai ƙarar Amazon ne saboda yadda kamfanin ya ke tafiyar da sayar da manhaja a rumbun Kindle

Wani alkali a Amurka ya zartar hukunci cewa kamfanin Amazon ya riƙa sayar da manhaja da aka yi don ƙananan yara ga iyayen su ba tare da izni ba tsakanin 2011 zuwa 2014.

A shekarar 2014 ne hukumar dake kula da harkokin cinikayya a Amurka ta kai ƙarar Amazon saboda yadda kamfanin ya ke tafiyar da sayar da manhaja a rumbun Kindle da kuma wayoyin komai da ruwan ka.

Hukumar dai ta sasanta a wajen kotu tsakanin ta da Apple da kuma Google dangane da rumbun sayar da manhajoji a shekarar.

Hukumar ta ce za ta buƙaci kotu da ta nemi a biya daukacin mutanen da lamarin ya shafe su wadanda ke ciniki da Amazon.