Ana samun karuwar satar mutane a Kano

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Babban sifetan 'yan sandan Najeriya Solomon Arase

Satar mutane don neman kudin fansa na kara zama wata babbar matsalar tsaro a jihar Kano da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ke kara jefa rayuwar mazauna yankunan cikin fargaba.

Matsalar dai ta fi kamari ne a kudancin jihar da ke makwabtaka da dajin Falgore wanda ke hade da wasu manyan dazuzzuka a yammacin Afrika, dazukan da suka zama tamkar mazauni ga masu aikata miyagun laifuka.

Baya ga Jihar Kano, jihar Kaduna ma na fuskantar wannan matsala ta satar mutane don neman kudin fansa.

A farkon watan Aprilu ne babban sipeton 'yan sanda Najeriyar Solomon Arase ya umurci mataimakin shugaban 'yan sanda AIG na shiyya ta 7 AIG Ballah Nasarawa da ya koma Kaduna har sai al'amurran tsaro sun inganta a jihar.