Zabiya na fuskantar barazanar karewa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana tsafi da bangarorin jikin Zabiya a kasashen gabashi da kuma kudancin Afrika

Wata kwararriya a majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa zabiyan da su ke kasar Malawi na cikin hadarin a kawar da su daga doron kasa.

Ikponwosa Ero ta ce zabiya dubu 10 na kasar suna cikin hadari saboda ana kashe akasarinsu.

A na amfani da bangarorin jikinsu wurin yin tsafi saboda 'yan kasar sun yi amannar hakan na kawo sa'a da arziki.

'Yan sandan Malawi sun samu kararraki na hare-hare da na sace-sace da kuma kashe-kashen zabiya 65 tun karshen shekarar 2014.

Ana kashe zabiya a wasu bangarorin gabashi da kuma kudancin Afrika, har ma da da kasar Mozambik da Tanzania saboda wadancan dalilan.