Buhari ya yi fushi kan rashin biyan albashi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana matukar rashin jin dadinsa a kan kasa iya biyan albashin ma'aikata da kashi biyu cikin uku na jihohin kasar suka yi duk kuwa da kudin da ya basu domin su iya biyan albashin.

Shugaban ya fadi haka ne a taron da ya yi da gwamnonin jihohin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya ce yana matukar jin takaici saboda halin da rashin biyan albashin ya jefa ma'aikatan jihohon da iyalansu.

Gwamnonin dai sun shaida masa cewa sun kasa biyan albashin ne saboda halin tabarbarewar da tattalin arzikin kasar ya fada saboda faduwar farashin man fetur da kuma zargin sace kudaden da gwamnatin da ta gabata ta yi.

Shugaban kungiyar gwamnonin, AbdulAziz Yari, ya yi wa Haruna Tangaza karin bayani kan dalilinsu na neman a ba su kudi:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaba Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta biya gwamnatocin jihohin wasu kudade da suke bin ta sakamakon ayyukan gwamnatin tarayya da suka yi a jihohin domin su samu damar biyan albashin.