Saudiya: Kamfanin Binladen ya rage ma'aikata 50,000

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin Binladen mallakin dangin Osama Bin Laden

Daya daga cikin manyan kamfanonin da ke Saudiya Bin Laden Group, ya sallami ma'aikatansa dubu 50 yayin da gwamnati ke kokarin rage kashe kudi domin ta shawo kan faduwar farashin mai.

Kamfanin, wanda mallakin dangin Osama bin Laden ne, ya shafe shekaru yana samun kwantiragin gine-gine, wadanda suka hada da fadada masallacin harami daga masarautar Saudiya.

A lokacin da kamfanin Binladen din ke tashe, yana da ma'aikata dubu 200.

Yanzu dai an dakatar ko an fasa ayyukan gine-gine yayin da tattalin arzikin Saudiyan ke cigaba da fuskantar matsaloli.

Ma'aikatan dai sun sha yin zanga-zanga saboda rashin biyansu albashi da ake yi na watanni.