A gudanar da bincike kan harin Kunduz- MSF

Hakkin mallakar hoto MSF

Kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta yi kira a gudanar da bincike game da harin da jirgin yakin Amurka ya kai kan wani asibiti a Afghanistan.

Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane arba'in da biyu a asibitin dake Kunduz, inda kungiyar ta MSF ke gudanar da aikinta.

Rundunar sojin Amurka ta ce sojojinta sha shidda ne za a hukunta kan harin da aka kai a garin Kunduz, amma kuma ba za su fuskanci hukuncin aikata laifukan yaki.

Kungiyar ta MSF dai ta yi kiran da a hukunta su daidai da barna da kuma kisan rayukan da suka haddasa.

Sai dai Rundunar sojin Amurkar ta ce harin bai kai yadda za a kira shi da laifin yaki ba, saboda dakarun na zaton sun kai harin ne kan helkwatar mayakan Taliban a Kunduz ba a asibiti ba.

Su ma dai 'yan kasar ta Afghanistan da suka tsira daga harin sun yi kira da cewa wadanda ke da hannu su fuskanci hukuncin.