Gwamnati ta ce a kama mai ginin da ya rufta a Kenya

Image caption Mutane bakwai sun mutu bayan gini ya rufta a Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayar da umurnin a kama mai ginin da ya rufta a Nairobi babban birnin kasar wanda ya yi sanadin mutuwar mutum akalla bakwai.

Mr Kenyatta wanda ya ziyarci wajen da abin ya faru, ya ce gine-ginen da ke kusa da wanda ya rufta ma ba su da tabbas dan za su iya ruftawa, a saboda haka ne ya bukaci mazauna gine-ginen da su tashi.

Aikin ceton mutanen da lamarin ya shafa na samun tsaiko saboda ruwan sama kamar da bakin kwaryar da ake yi, da kuma rashin samun manyan injinan da za a yi amfani da su wajen isa wajen.

Mahukunta sun ce tuni aka bayar da umarnin a rusa ginin mai shekaru biyu saboda bai cika ka'idojin da ya kamata ba.

An dai ceto mutane fiye da dama ciki har da kananan yara a baraguzan ginin da ya rufta.