Mutane tara sun mutu a Somaliya

Hakkin mallakar hoto gett
Image caption Mutane tara sun mutu a Masallacin Somaliya

Akalla mutane tara sun rasa rayukansu, yayinda wasu da dama kuma suka jikkata bayan da wani masallaci ya rufta a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.

Yawancin wadanda suka mutun ma'aikata ne wadanda ke aikin gyaran ginin masallacin da ke arewacin birnin.

Lamarin ya faru ne a dai-dai lokacin da mutane fiye da dari ke zuba kankare a tubalin ginin.

Rahotanni sun ce tuni aka bayar da umurnin kama Injiniyan da ke kula da ginin masallacin saboda sakacin da ya yi a aikin ginin.