Nigeria: INEC ta dakatar da zabe a Minjibir

Hakkin mallakar hoto Channels TV
Image caption An dakatar da zaben karamar hukumar Minjibir

Hukumar zabe a Najeriya ta sanar da dakatar da zaben maye gurbi na dan majalisar jihar da aka gudanar a ranar Asabar a karamar hukumar Minjibir.

Hakan dai ya biyo bayan rikicin da ya barke a tsakanin magoya bayan jam'iyyu, al'amarin da ya janyo rasa rayuka da kuma jikkata.

Ana dai gudanar da zaben ne sakamakon rasuwar da dan majalisar da ke wakiltar karamar hukumar ta Minjibir Alh Hamisu Garba Gurjiya ya yi a watannin baya.

Nick Dazang shi ne kakakin hukumar zabe ta Najeriya ya yi wa Aisha Shariff Baffa karin bayani ta wayar tarho.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti