Nigeria: 'Za mu kare mutuncin fulani makiyaya'

Hakkin mallakar hoto State House

A Najeriya gwamnonin arewacin kasar sun nuna damuwa a bisa kashe kashen daya wakana a Agatu na jahar Benue da kuma na jahar Enugu.

Gwamnonin na arewa wadanda suka ce sun tattauna wannan batu a taron da suka yi a Kaduna, sun kuma nuna takaicin su dangane da yadda wasu ke dora alhakin kashe kashen a kan Fulani makiyaya .

A ganin gwamnonin dora tsana da kiyayya a kan wata kabila ba wata hujja kwakkwara ,ba zai tabbatar da hadin kai da zamantakewa ta gari da ake bukata a kasar ba.

Gwamnan jahar Borno Alh Kashim Shettima, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin na arewa ya shaidawa wakilin mu na Kaduna Nurah Mohammed Ringim bayan taron na su a Kaduna cewa a matsayin fulani 'yan kasa dole ne su kare mutuncin su.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti