Adadin wadanda suka mutu a Kenya ya karu

Image caption wadanda suka mutu sakamakon ruftawar ginin a Nairobi sun karu zuwa 14

Mahukunta a kasar Kenya sun ce ya zuwa yanzu mutane akalla goma sha hudu ne suka rasa rayukansu bayan da wani gini ya rufta a ranar Jumm'ar da ta gabata sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya da aka yi a Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Ana dai cigaba da aikin ceto,sai dai kuma ba a amfani da injin da ake zakulo kasa saboda gudun kada a jiwa wadanda ba su mutu ba da ke karkashin kasa ciwo.

Har yanzu dai ba a ga wasu mutanen ba, ko da yake wasu daga cikin mazauna ginin ba sa nan a lokacin da lamarin ya faru.

Gwamnan Nairobi Evans Kidero ya ce za a tuhumi wadanda suka amince da yin ginin a wajen.