Nigeria: Dole a ƙara wa ma'aikata albashi — NLC

Image caption Kungiyar kwadago a Najeriya ta ce dole a kara albashin ma'aikata

Ƙungiyar kwadago ta ƙasa a Najeriya wato ta nemi a ƙarawa ma'aikata yawan albashin da suke ƙarba daga naira 18,000 mafi ƙaranci zuwa dubu naira 56,000.

Ƙungiyar ta yi wannan kira ne bisa la'akari da tsadar rayuwa da kuma wahalhalun da ma'aikata suke fuskanta.

NLC ta yi wannan kira ne a bikin ranar ma'aikta ta duniya da aka yi ranar Lahadi.

Usman Minjibir ya tattauna da Comrade Nuhu Abbayo Toro, mataimakin kakakin ƙwadago ta kasa a Najeriya kuma ya soma da tambayarsa shin ko menene ya ja ra'ayinsu kan wannan batu?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti