Somalia:Al-Shabaab ta kwace kauyen Runorgood

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar al Shabaab ta ce ta kashe sojojin gwamnati fiye da 30 lokacin da suka sake karbe kauyen Runorgood da ke arewa maso gabashin Mogadishu babban birnin kasar.

Babu dai wani martani daga rundunar sojin Somalia.

Mazauna yankin sun tabbatar wa da BBC cewa lallai yan al Shabaab sun karbe iko da kauyen Runorgood.

A jiya Asabar aka fatattaki yan bindigar amma kuma suka sake karbe iko da kauyen a yau Lahadi.

A waje guda kuma a kalla mutane uku suka rasa rayukansu a wani harin bam a wata kasuwar dabbobi a Qoryoolay wanda ake kyautata zato an hari ma'aikatan haraji ne na gwamnati.