Syria: Tattaunawar tsagaita wuta a Aleppo

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani jami'in ma'aikatar tsaron Rasha yace shawarwari na gudana domin samar da abin da ya kira tsagaita hare hare a arewacin birnin Aleppo a Syria da ake gwabza fada.

Kalaman na Laftanar Janar Sergei Kuralenko ya nuna sauyin ra'ayi kan matsayin Rasha.

A ranar Asabar, Moscow ta ce ba za ta tilasta wa sojojin Syria dakatar da farmakin da suke yi ba.

Fararen hula fiye da 250 aka kashe a birnin a kwanaki goma da suka wuce.

Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai isa Geneva domin tattauna halin da ake ciki tare da Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura da kuma ministocin harkokin waje na kasashen Jordan da Saudiyya.