An toshe WhatsApp a Brazil

Hakkin mallakar hoto EPA

Wani alƙali a Brazil ya bada umarnin toshe hanyar sadarwar wayar salula ta Whatspp na tsawon awa 72.

Alkalin Marcel Montalvao ya ce, kamfanin WhatsApp ya ƙi miƙa wani bayani da ake buƙata domin binciken wani laifi da aka aikata.

Koda a watan Maris alkalin ya bada umarnin kama babban jami'in kamfanin Facebook mai kula da kasashen Latin Amurka saboda ya ƙi bada haɗin kai a wani binciken da ya shafi safarar mayagun ƙwayoyi.

Kamfanin WhatsApp wanda mallakar Facebook ne ya bayyana takaici dangane da matakin da alƙalin ya ɗauka.

Cikin 'yan watannin da suka gabata dai an sha toshe WhatsApp a ƙasar ta Brazil.