Kwayoyin halitta na janyo sankarar mama

Wata kungiyar masana kimiyya ta kasa da kasa ta kammala bincike mafi girma na kwayoyin halittar gado na sankarar mama, wanda suka ce ya basu asalin dalilin da ke kawo cutar.

Masana kimiyyar sun bincika dukka taswirar kwayoyin halittar sama da mutane dari 5 dake dauke da sankarar mama.

Binciken, wanda cibiyar Sanda dake Cambridge ta jagoranta, ta gano wasu sabbin kwayoyin halittar gado 5 da ke da alaka da sankarar mama.

Wannan kuma ya kai adadin kwayoyin halittar gadon zuwa 93 da idan suka sauya, zai kai ga sankarar mama.

Daya daga cikin mutanan da suka gudanar da binciken ta ce suna ganin samun cikakken hoto da bayani zai taimaka wajan samar da magungunan cutar.