'Yan gudun hijira suna yin sana'oi

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu da ke zaune a sansanoni dabana-daban, na koyon sana'oi domin taimakawa kansu da kansu.

Wasu da ke zaune a garin Gumel na jihar Jigawa a Najeriya na daga cikin wadanda suka rungumi sana'oi domin dogaro da kai.

Da dama daga cikinsu sun koyi sana'o'i da suka dogara da su wajen biyan bukatunsu na yau da kullum.

Sana'o'in dai sun hada da sarrafa man wanke gashi, da sabulu, da dinke-dinke, da dai sauransu.

'Yan gudun hijirar maza da mata ne suka koyi sana'o'in.

Dubban jama'a ne suke zaman gudun hijira a sassa daban-daban sakamakon rikicin Boko Haram.