Taron biki ya zama na makoki a Nigeria

Image caption Ana yawan samun hatsarin mota a titunan Nigeria

Rahotanni daga jihar Gombe a arewacin Najeriya na cewa ana cigaba da zaman makoki a garuruwan Gombe da Kumo, bayan da wani mummunan hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane takwas masu bikin aure, cikinsu har da angon.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadi, yayin da angon ke tuka motar domin mayar da dangin amaryar gida bayan da aka kai ma shi amaryar.

Bayanai sun ce yayin da suka kusa isa garin na Kumo, sai motar ta kwace wa direban, ta yi karo da wata bishiya da ke gefen titi.

Ga rahoton da wakilinmu Ishaq Khalid ya aiko mana daga Bauchi:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti