Leicester City ya lashe gasar Premier

Hakkin mallakar hoto Reuters

Klob ɗin Leicester City ya lashe gasar Premier bayan Tottenham da Chelsea sun yi kunnen doki ci 2-2 a ranar Litinin.

Wannan nasara da Leicester ya yi, ta kara tabbatar da kokarin da mai horar da 'yan wasan klub din Claudio Ranieri ke yi.

A baya dai klob din ya kasa yin nasarar lashe wasan league sau uku.

A fagen kwallon kafa, ana kallon wannan nasara ta Leicester City a matsayin wani abin mamaki.

Ko da tsohon dan wasan Ingila, Gary Lineker, wanda dan Leicester ne, kuma ya soma kwallo a klob din ya ce, wannan nasara ce mai ban mamaki sosai.