Niger: Ministocin Faransa da Jamus na ziyara

Image caption Shugaban kasar Niger din Mahamadou Issoufou.

A jamhuriyar Nijar, a ranar Litinin ne Ministocin harkokin waje na kasashen Faransa da Jamus ke soma wata ziyarar aiki ta wuni biyu a kasar.

Ministocin biyu suna wani rangadi ne da tuni ya kai su kasar Mali.

A Nijar ne za su tattauna da hukumomi game da batutuwa da dama da suka hada da tsaro da matsalar bakin haure da samar da ruwa domin bunkasa ayyukan noma.

Ana kyautata zaton ziyarar dai za ta kara karfafa huldar da ke akwai tsakanin kasashen na Jamus da Faransa da kuma jamhuriyar ta Nijar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakilinmu a Yamai BARO ARZIKA ya tattauna da ministan harkokin wajen kasar ta Nijar, Alhaji Ibrahim Yakuba, domin jin karin bayani kan makasudin ziyarar.