Shin mutuwar Bin Laden ta bar darasi?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Osama Bin Laden shi ne shuagaban al-Qaeda, kuma sojojin Amurka sun kashe shi ne a shekarar 2011.

Ranar Litinin ne ranar da aka cika shekaru biyar cur tun da dakarun sojin Amurka suka kashe Osama bin Laden, a wani katafaren gida a Pakistan, mutumin da duniya ta dade tana neman ruwa a jallo.

Ga Amurka, wannan aiki da aka gudanar cikin sirri, ba tare da sanin gwamnatin Pakistan ba, ya zamo wa kasar tamkar ramuwar gayya ga harin da aka kai mata ranar 9 ga watan Satumbar shekarar 2001.

Ga Pakistan kuwa, wannan lamari ya kunyata kasar kuma sun dauke shi da zafi, ganin yadda aka gano cewa Bin Laden, ko kuma 'OBL' kamar yadda turawa suka masa lakani, na zaune cikin daula Mil 31 kacal daga Islamabad, babban birnin kasar, kuma bugu da kari kusa da makarantar sojin Pakistan da ke Abbottabad.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An gano maboyar Shugaban na al-Qaeda zuwa wani gidan sa da ke Abbottabad.

A bara an samu hare-haren da ke da alaka da ta'addancin a kusan kowacce nahiya, an samu a Turai da Amurka da Gabas Ta Tsakiya da Kudu maso gabashin Asiya da kuma Afrika.

To cikin hare-haren da ake samu, guda nawa ne suka dauki darasi daga ayyukan Osama Bin Laden kuma wace matsala ce ta da sa tushe na dogon zango ga duniya?

"Rasuwar Bin Laden ta bar darasi kam," In ji Dr Sajjan Gohel, na gidauniyar Pacific Foundation.

Ya kara da cewa, "amma a wani gefen, ISIS ta masa zagon kasa, inda suka kara kan darussan da ya bari, domin cimma burin kafa daular musulunci a duniya."

Ga wasu mutanen, shekaru 22 da kungiyar Alqa'idar Bin Laden ta yi tana mulki daga shekarar 1989 zuwa shekarar 2011, ba shi da wani bambanci da akidar ta'addancin kungiyar IS a yanzu.

Duk kungiyoyin biyu sun dauki wani tunani na daban ne, da tattsauran ra'ayi ga duk wanda baya ra'ayinsu, sun kuma amince da cewa Dimokradiyya ba ta da gurbi a tsarin shari'ar musulunci.

Amma kuma akwai bambanci tsakaninsu, don kuwa idan da OBL na nan a raye yau, da ya soki ta'asar da IS ke aikatawa.

Tsarin Bin Laden ya hada ne da hakuri da hangen nesa, inda ya so karya lagon Amurka da Turai da hare-haren da zai tilasta masu janye goyon baya da su ke baiwa shugabannin Gabas Ta Tsakiya, domin masu kishin islama su samu damar kafa daular musulunci.

Osama dai ya yi wa wannan buri kallon na dogon zango, kuma ba lallai ne mai yiwuwa a rayuwarsa ba.

Ko kafin rasuwarsa, akwai alamu da suka nuna cewa Osama da shugabannin Al-qaeda da ke Pakistan, ba su amince da ta'asar da sashen Al-Qaeda da ke Iraki ke aiwatarwa ba, kuma a yau sune suka rikide suka zama kungiyar IS.

An haifi Osama Bin Laden a shekarar 1957, kuma shi ne na 17 cikin yara 52 ga iyalan Mohamed Bin Laden, wani attajiri da ke da ya aiwatar da ayyukan kwangilolin gina fiye da kashi 80 cikin dari na titunan Saudiyya.

Bayan mahaifinsa ya rasu a wani hadarin jirgi mai saukar ungulu a shekarar 1968, Osama ya yi gadon miliyoyin daloli.

Ya samu tsattsaurar ra'ayi lokacin da yake karatun Injiniya a jami'ar King Abdul Aziz da ke Jidda, a Saudiyya.

Osama ne aka dora wa alhakin harin benen cibiyar kasuwanci ta duniya - World Trade Center da ke New York da fashewar wani bam a cikin wata mota a shekarar 1995 a tsakiyar Riyadh babban birnin Saudiyya da wani bam kuma da ya tashi cikin wani a kori - kura da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 19.

Kazalika Osama ya bayar da fatawa a watan Fabrairun 1998, inda ya ce hakkin kowanne musulmi ne ya kashe Amurkawa da magoya bayansu.

A kwanakin nan, dan takarar Amurka Donald Trump ya sha alwashin murkushe kungiyar ta IS, amma bai fadi ko ta yaya zai cimma wannan burin ba.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar ta IS ta fi daukakn tsattsaurar matakai, fiye ma da kungiyar al-Qaedar Bin Laden.

Duniya dai ta hada kai wajen yunkurin an kawo tsagaita yaduwar masu tsattsaurar ra'ayin addinin musulinci, kuma rashin shugaba mai kwar jini irin OBL ba zai bayar da damar samun sa'idar da mutuwar sa shekaru biyar da suka gabata ya janyo ba.