Paul Biya yana ziyara a Nigeria

A ranar Talata ne shugaban Kamaru Paul Biya ke yin wata ziyara a Najeriya bisa gayyatar shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasar Najeriya ta ce za a tarbi tawagar Shugaba Paul Biya da suka hada da mai dakinsa, Chantal, da kuma wasu manyan jami'an gwamnati, a fadar shugaban kasa ta Aso rock Villa da ke Abuja, babban birnin kasar.

Mai taimakawa shugaban kasar na musamman a kan watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya yi wa BBC karin bayani kan ziyarar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugabannin biyu da jami'an gwamnatocinsu za su tattauna kan batutuwan da suka hada da tsaro da yaki da ta'addanci da suka addabi kasashen biyu da kuma laifukan da ake aikatawa a kan iyakokin kasashen biyu.

Ana sa ran shugabannin biyu za su sanya hannu a kan yarjejeniyar da za ta kara dankon zumunci tsakanin kasashensu, wadanda za su karfafa kasuwanci da tattalin arziki.