Kayan Reckitt Benckiser sun kashe mutane a Koriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban kamfanin ya nemi afuwar 'yan Koriya ta Kudun

Wani kamfanin Burtaniya, Reckitt Benckiser, ya amsa cewa daya daga cikin kayayyakinsa ya haddasa mutuwa da jikkatar mutane da dama a Koriya Ta Kudu.

Da yake magana a wajen wani taron manema labarai wanda 'yan uwan mutanen da lamarin ya shafa da suka halarta cike da bakin ciki, shugaban reshen kamfanin a Koriya, Ataur Safdar, ya ce ya yi nadamar abin da ya faru kuma ya bayar da hakuri.

Matsololin sun taso ne daga na'urar daidaita danshin daki, wanda mahukuntan Koriya ta Kudun suka ce sinadaran na'urar ne suka haddasa a shekara ta 2011.

Sai dai kungiyar masu goyon bayan wadanda lamarin ya shafa sun ce ba sa bukatar nadamar kamfanin, suna so ne a rufe kamfanin a kasar.