Ranar 'yan cin 'yan jarida ta duniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters

A yau ne 3 ga watan Mayu , kuma rana ce da ake bikin 'yan cin 'yan jarida ta duniya baki daya.

Majalisar dinkin duniya ce ta kebe ranar kowacce shekara domin fadakar da jama'a illolin hana kafafen yada labarai tsage gaskiya .

Kuma a baiyana irin muzgunawar da ma wani lokaci kisa da 'yan jarida ke fuskanci a cikin aikin su na nema da watsa labarai.

A kasar jumhuriyar Nijar, lamarin aikin jarida na cikin wani hali na tsaka mai wuya.

Game da tsangwamar da 'yan jarida ke fuskanta, Nijar na ta 47 a bara, bana kuma ta 52 kamar yadda rahoton kungiyar kare hakin 'yan jarida ta duniya ta kasar Faransa Reporter Sans Frontiere ta sanar.