Hadarin Zika ya fi yadda aka tsammanta — Likitoci

Image caption Sauro ne ke yada cutar zika

Masana kimiyya a Brazil sun ce cutar Zika wadda sauro ke yadawa na da matukar hadari fiye da yadda aka zata tun farko.

Sun shaidawa BBC cewa, Zika na iya zama sanadin lalata yanayin wani bangare na kwakwalwa, inda hakan ke shafar jarirai kusan kashi biyar na matan da ke dauke da juna biyu.

Karuwar yaduwar Zika a wasu bangarori na Brazil ya ragu, sakamakon samun bayanai kan kare yaduwar cutar.

Amma har yanzu ba a yi nisa wajen neman riga-kafin cutar ba.

Kuma cutar Zika na cigaba da yaduwa a wannan yanki.