Baƙin Haure: Nijar ta nemi tallafi

Hakkin mallakar hoto Reuters

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ce tana buƙatar Euro biliyan guda domin yaƙi da matsalar baƙin haure.

Ministan harkokin wajen Nijar, Ibrahim Yacouba ne ya gabatar da bukatar kudaden yayin ganawa da takwarorinsa na Faransa da Jamus yayin ziyararsu a Nijar.

Nijar dai ta kasance hanyar da baƙin haure 'yan Afirka suke bi domin tsallakawa Turai.

Bakin haure fiye da dubu ɗari ne suke ratsawa ta cikin Nijar a kan hanyarsu ta shiga Turai a kowacce shekara.

Koda bara kasashen Turai sun samar da fiye da Euro biliyan guda ga ƙasashen yammacin Afirka domin shawo kan matsalar baƙin haure.

Amma shugabannin kasashen Afirka dai sun ce, suna bukatar karin kudade domin fuskantar matsalar ta bakin haure.