Yunkurin samar da zaman lafiya a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fararen hula na ci gaba da tserewa daga Syria.

Wakilin majalisar dinkin duniya na musamman a Syria, Staffan de Mistura, ya je Moscow domin tattaunawa da ministan hulda da kasashen waje Sergei Lavrov dangane da yadda za a farfado da tsagaita wuta a Syria.

Hari ta sama da aka kai a birnin Aleppo na arewacin Syria ya kusa kawo karshen tsagaita wutar da aka cimma cikin watan Fabrairu.

Gwamnatin Syria da Rasha sun ce an kai hari a Aleppo ne da nufin samun mayakan kungiyar Al Nusra, wadda take da alaka da Al Qaeda.

Sai dai 'yan tawaye da Amurka sun yi watsi da wannan dalili da gwamnatin Syria da Rasha suka bayar.

Hakan na faruwa ne a daida lokacin da Majalisar Tarayyar Turai ta ce za ta bai wa 'yan kasar Turkiyya damar shiga Turai saboda taimako da take bayar wa wajen tsugunar da 'yan gudun hijirar da suka guje daga Syria.

BBC ta fahimci cewa majalisar Turan za ta dauki wannan mataki ne idan Turkiyya ta cika wasu sharuda da aka gindaya mata.