Trump na dab da zama ɗan takarar Republican

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Babu wanda ya dauki Trump da muhimmanci lokacin da ya fara yakin neman zabe.

Donald Trump ya zama mutumin da zai yi wa jam'iyar Republican takarar shugabancin Amurka bayan kayen da ya yi wa abokin takararsa Ted Cruz a zaɓen fitar da gwani na jihar Indiana ya tilasta masa janyewa daga yin takarar.

Yanzu dai Mr Trump, wanda ba shi da farin jini a wajen 'yan jam'iyyar, ya share hanyar samun wakilai 1,237 da ake buƙata domin tsayawa takarar shugabancin ƙasar.

Hakan dai wani abin mamaki ne, ganin cewa mutanen ba su dauke shi da muhimmanci ba a lokacin da ya fara yakin neman zabe a bara.

Bernie Sanders ya doke Hillary Clinton a zaben fitar da gwani na jam'iyyar Democratic a jihar ta Indiana.

Sai dai har yanzu ita ce ke gaba a yawan jihohin da suka lashe.

Ya ce Clinton tana tunanin an kammala yakin neman zaɓe, yana mai cewa hakan kuskure ne.

Karin bayani