Wani yaro ya gano kuskure a Instagram

An bai wa wani yaro dan kasar Finland mai shekaru 10 mai suna Jani dala 10,00 bayan ya gano wani kuskure a wajen musayar hotuna a manhajar Instagram.

Bayan ya gano kuskuren a watan Faburairu, sai ya aikewa kamfanin Facebook sako ta intanet ya gaya musu.

Injiniyoyin da ke kula da tsaro na kamfanin Facebook sun yi masa gwaji domin ya tabbatar da kuskuren da ya gano.

Yaron, wanda bai kai shekarun da suka kamata a ce ya shiga manhajar ta Instagram ba har sai shekaru uku nan gaba, ya gano wata na'ura da ta ba shi damar goge ra'ayoyin da wasu masu amfani da manhajar suka yi.

Kamfanin Facebook, wanda shi ke da manhajar ta instagram, ya shawo kan lamarin da wuri bayan an gano kuskuren.

Ba tare da bata lokaci ba aka biya Jani kudi, wanda hakan ya sa ya zamo mutun mafi karancin shekaru da ya taba karbar irin wannan kyautar ta "bug bounty".